Bongo ya shaidawa radiyon kasar Faransa na RTL cewa, ba zai karya doka ba. A cewarsa kotun tsarin mulki kasa ce kadai ke da ikon ba da umarnin sake kidiya kuri'un da aka kada.
A makon da ya gabata ne dai rikici ya barke a kasar da ke tsakiyar Afirka, bayan da 'yan adawa suka nuna rashin amincewa da sakamakon zaben da ya baiwa shugaba Bongo nasarar sabon wa'adin mulki na tsawon shekaru 7.
Rahotanni na cewa, tashin hankalin da ya barke a kasar yayi sanadiyar mutuwar mutane 3 kana wasu daruruwa suka jikkata.(Ibrahim)