in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Gabon da abokin takararsa sun kai kara a gaban kotu
2016-09-09 12:33:42 cri

A jiya Alhamis ne, shugaban kasar Gabon Ali-Ben Bongo Ondimba da dan takarar 'yan adawa Jean Ping suka shigar da kara a gaban kotun tsarin mulkin kasar , inda suka zargi juna da tabka magudi a zaben da aka yi a ran 27 ga watan Agusta.

Ali-Ben Bongo Ondimba ya shigar da kara a wannan rana yana zargin Jean Ping da tafka magudi a lokacin zabe.

A nashi bangare kuwa, Jean Ping ya nuna rashin jin dadi kan sakamakon zabe, kuma ya neman kotun da ta sake kirga kuri'un da aka kada a garin Bongo wato jihar Haut-Ogooue.

A ran 31 ga watan Agusta hukumar zabe ta kasar Gabon ta bayyana sakamakon zabe cewa, dan takara jam'iyyar Dimokuradiyya kuma shugaba mai ci Ali-Ben Bongo Ondimba ya lashe zabe bisa rinjaye kadan. Daga baya kuma, wasu masu zanga-zanga sun cinna wuta a birnin Libreville hedkwatar kasar tare da yin arangama da rundunar tsaron kasar. Magoya bayan Jean Ping sun sanar da cewa, kuri'un da Jean Ping ya samu ya fi na Bongo yawa, kuma sun ki amincewa da Bongo da ya yi tazarce tare da neman a sake kididdiga kan kuri'u. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China