in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gabon: Ali Bongo ya lashe zaben shugaban kasa da kashi fiye da 50,6 cikin 100
2016-09-24 17:09:22 cri
Kotun tsarin mulkin kasar Gabon ta sanar da sanyin safiyar yau cewa Ali Bongo, shugaban mai barin gado, ya sake lashe zabe da kashi fiye da 50,6 cikin 100 na kuri'un da aka jefa.

Bayan nasasar Ali Bongo da ta janyo cece kuce da ma'aikatar cikin gida ta sanar a cibiyar hukumar zabe mai zaman kanta ta CENAP a ranar 31 ga watan Augusta, babban dan adawar nan Jean Ping ya gabatar da kara inda ya nemi da a sake kidayar kuri'un zabe na kowace rumfar zabe, musammun ma a yankin Haut-Ogooue, inda Ali Bongo ya samu kashi fiye da 95 cikin 100 na kuri'un da aka jefa, tare da kashi fiye da 99 cikin 100 na halartar zaben. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China