in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na ci gaba da tallafawa bangaren ilimi a Nijeriya
2017-09-30 13:04:03 cri
Kasar Sin ta mika wasu sabbin ajujuwa da aka gina da kayakin karatu da darajarsu ta Naira miliyan 20, kwatankwacin dala dubu 56,000 ga Gwamnatin jihar Lagos dake kudu maso yammacin kasar.

Kamfanin gine-gine na China Civil Engineering Construction Corporation ne ya gina ajujuwa da babban wakilin kasar Sin a Nijeriya ya dauki nauyi ta hannun kungiyar kawance ta al'ummomin kasar Sin da kasashen Afrika.

An sanyawa ajujuwan da aka fara gininsu a watan Yunin da ya gabata, tebura da kujeru da alluna irin na zamani da kuma fankoki domin jin dadin dalibai da malamai.

Mataimakin babban wakilin kasar Sin a jihar Lagos Guan Zhongqi, shi ne ya mika ajujuwan dake harabar makarantar Iwora Ajido na yankin Badagry, ga Gwamnatin jihar.

Wakilin ya ce an bada tallafin ne, domin inganta aminci tsakanin kasar Sin da Nijeriya tare da bunkasa ingancin ilimi a kasar, ya na mai cewa aikin na da muhimmanci ga hadin gwiwar kasar Sin da Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China