Major Ibrahim Abdullahi, shi ne mai Magana da yawun rundunar sojin, ya shedawa 'yan jaridu a Yenagoa babban birnin jahar Bayelsa mai arzikin mai cewa, bayan sojojin da aka ceto, an kuma ceto wasu fararen hula su 4 a lokacin da dakarun sojojin suka kaddamar da aikin sintiri.
Ya ce sakamakon barin wuta da rundunar sojin suka kaddamar an samu hasarar rayukan wasu daga cikin masu garkuwar yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu inda suka shiga cikin dazuka.
Abdullahi yace daga cikin kayayyakin da sojojin suka gano a sansanin tsagerun sun hada da wasu manyan bindigogi 3, da emtin kwanson alburusai guda 8 dauke da kokon kan mutane da wasu kasusuwa.