in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta amince da haramta kungiyar 'yan a-ware ta kasar
2017-09-21 09:13:36 cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya amince da matakin haramta kungiyar fafutukar kafa Jamhuriyar Biafra wato IPOB.

Ministan yada labaran kasar Lai Mohammed, wanda ya bayyana haka jiya a Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce kungiyar ta rubuta wasika ga kasashen yamma inda take mai zargin ana aiwatar da kisan kiyashi a yankin kudu maso gabashin kasar.

Lai Mohammed ya ce, ko wane mutum ko kungiya na da 'yancin zabar yankin da yake son kasancewa, sai dai dole ne yunkurin ya zama bisa doron doka kuma cikin kwanciyar hankali.

Ya kara da cewa, IPOB wata kungiya ce dake adawa da Gwamnatin Buhari, wanda kuma hadakar 'yan siyasa da wadanda suka yi sama da fadi da kudaden al'umma ke daukar nauyinta.

Ministan ya ci gaba da cewa, IPOB ta yanke shawarar kai kokenta ga kasashen waje ta hanyar rubutawa gwamnatocin kasashen yamma da majalisun dokokinsu, tana mai ikirarin ana mata kisa kiyashi tare da amfani da faifan bidiyon karya na kashe-kashe domin yaudarar mutane.

A cewarsa, IPOB ta fara wani yunkuri na diflomasiyya, inda ta kafa hedkwatar harkokinta na kudi a kasar Faransa tare da tashar rediyo a birnin London, yana mai cewa, gwamnatin Nijeriya za ta datse hanyoyinta na samun kudi daga ketare.

A ranar Jumma'a da ta gabata ne hedkwatar tsaron Nijeriya ta ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta'addanci, kana tana mai bukatar iyaye su hana 'ya'yensu shiga cikinta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China