in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: Yawan marasa ilimi a Nijeriya abu ne mai ta da hankali
2017-09-22 09:54:57 cri

Ministan ilimin Nijeriya Adamu Adamu, ya yi gargadi game da yadda matsalar rashin ilimi ta yi yawa a kasar, yana mai cewa, matsalar ta shafi mutane miliyan 75 daga cikin sama da mutane miliyan 180, adadin da ya kai kashi 41 na al'ummar kasar.

Da yake jawabi a jihar Kebbi dake arewacin kasar yayin wata ziyarar da ya kai wa gwamnan jihar Atiku Bagudu, Adamu Adamu ya ce, adadin ya yi yawa, yana mai bayyana shi a matsayin wanda bai dace ba, la'akari da yawan al'ummar kasar.

Ministan ya ce, gwamnatin Tarayya kasar ta mai da hankali kan yaran da ba sa zuwa makaranta, yana mai cewa, wannan wani bangare ne na muhimmin shirin gwamnatin na rage yawan marasa ilimi a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China