Asinim Butswat, kakakin rundunar 'yan sandan jahar Bayelsa ya tabbatar da afkuwar lamarin, yace wani dan sanda guda ya bace a lokacin kaddamar da harin.
A cewarsa, tuni aka tura jami'an gudanar da bincike don gano dan sanda da ya bace, kana dukkan jami'an tsaro a karamar hukumar Ijaw na zaune cikin shirinn ko-ta-kwana sakamakon faruwar lamarin.
Kwale-kwalen wanda ke dauke da tawagar jami'an tsaro da fararen hula wadanda ke yin rakiya ga babban jirgin ruwan dake dakon danyen mai, an kaddamar da harin kansa ne a ranar Juma'ar data gabata, harin da ake zargin masu fashin jirgin ruwa da kaddamarwa a kan tekun Ekebiri dake kudancin karamar hukumar Ijaw a jahar Bayelsa.
Mai Magana da yawun 'yan sandan ya shedawa 'yan jaridu cewa tuni aka tura jami'an kai dauki zuwa wajen da lamarin ya faru, kuma sun yi nasarar ceto 8 daga cikin mutanen da aka illata a cikin kwale kwalen.
Wannan harin ya zo ne makonni 3 bayan wani musayar wuta da aka yi a wani gidan sojoji dake kan tekun, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 2 a kudancin karamar hukumar ta Ijaw.