in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka na nazari game da rufe ofishin jakadancinta dake Cuba
2017-09-18 10:17:53 cri
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce kasar na duba yiyuwar rufe ofishin jakadancinta dake Cuba ko akasin haka, bayan wasu jami'anta sun kamu da rashin lafiya.

Rex Tillerson ya ce suna kan nazarin batun domin yana da muhimmanci gaya, la'akari da illar da ya yi wa wasu mutane, inda ya ce sun mai da wasu daga cikinsu gida.

Daga bisani hukumomin Amurkan sun tabbatar da cewa, Amurkawa a kalla 21 ne suka yi fama da alamomin cuta.

Babu cikakken bayani da aka fitar game da cutar, sai dai kafafen yada labarai sun ruwaito cewa wasu daga cikin Amurkawan sun gamu da lalurar ji, yayin da a kalla mutum guda gamu da matsala a kwakwalwa.

A watan Yulin 2015 ne Amurka da Cuba suka farfado da huldar diflomasiyya a tsakaninsu, bayan ya shafe sama da shekaru 50 cikin mawuyacin hali. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China