in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Amurka ta sanar da shirinta na sassauta tsimin dala trillion 4.5
2017-09-21 10:43:48 cri
Sashen tsimi na gwamnati Amurka yace tsarin kudin ruwan kasar ba zai sauya ba, amma ya bada sanarwar cewa zai sassauta tsarin ajiyarsa na dala trillion 4.5 daga watan Oktoba, a matsayin wani mataki da zai kawo karshen hasarar da kasar ke tafkawa a fannin harkokin kudinta.

An samar da wannan bayanai ne tun lokacin da kwamitin kula da harkokin kasuwan na gwamnatin tarayya yayi wata ganawa a watan Yuli inda ya nuna cewa guraben samar da ayyukan yi na kasar suna cigaba da samun tagomashi, kuma harkokin tattalin arzikin kasar yana samun matsakaicin cigaba a cikin shekarar bana. Amurkar ta sanar da hakan ne bayan kammala wani taron yini biyu kan sha'anin kudin kasar a ranar Laraba.

Mahukunta kasar ta Amurka suna fatar cigaban tattalin arzikin kasar zai cigaba da bunkasa cikin matsakaicin yanayi a nan gaba.

A bisa hasashen karuwar tattalin arzikin da gwamnatin kasar tayi wanda aka fitar da rahoton a ranar Laraba, jami'an gwamnatin Amurkar sun yi hasashe samun karuwar tattalin arzikin kasar da kashi 2.4 cikin 100 a wannan shekara, sama da hasashen kashi 2.2 cikin 100 da aka yi a watan Yuni.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China