Hanyar tattara kudin mai suna Invest4Climate wato zuba jari a sauyin yanayi, zata janyo hankalin masu zuba jari, kuma zata yi tasiri tare da samar da damammaki ga kasashe masu tasowa, musamman wajen samar da gagarumin cigaba na samar da manyan batura masu adana makamashi, da motoci masu amfani da lantarki, da kuma samar da na'urorin sanyaya gida wadanda basa fitar da sinadarai masu gurbata muhalli.
Shirin zai kuma taimaka wajen samar da zuba jari ta hanyar rage fuskantar gamuwa da haddura a sanadiyyar cigaba, daidai da irin bukatar da ake da ita, kuma shirin zai yi aiki tare da gwamnatocin kasashen duniya wajen inganta manufofin kare muhalli.(Ahmad Fagam)