in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar Conservative da jam'iyyar Democratic Unionists za su kafa gwamnatin hadin-gwiwa a Birtaniya
2017-06-10 13:14:03 cri
An kammala aikin kidaya kuri'un babban zaben kasar Birtaniya a Jiya Jumma'a, inda sakamakon zaben ya nuna cewa, jam'iyyar Conservative ba ta samu rinjayen kuri'u a majalisar dokokin kasar ba, al'amarin da ya sa, ba za ta iya kafa gwammnati ita kadai ba.

Firaministar Birtaniya Theresa May ce ta sanar da cewa, jam'iyyar Conservative da jam'iyyar Democratic Unionists za su kafa gwamnatin hadin-gwiwa.

Theresa May ta sanar da hakan ne bayan da ta gana da sarauniyar Ingila kana ta samu izinin kafa gwamnatin.

May ta alkawarta cewa, kafin gudanar da shawarwari kan ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai, gwamnatin hadin-gwiwa da za'a kafa, za ta tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Birtaniyar, da jagorantar baki dayan kasar ga samun ci gaba.

Jam'iyyar Democratic Unionists, jam'iyyar siyasa ce mafi girma a Northern Ireland, wadda ke da alaka ta kut da kut da jam'iyyar Conservative, haka kuma, tana son ci gaba da kasancewa a karkashin kasar Birtaniya.

Shi dai Shugaban jam'iyyar Democratic Unionists ya taba nuna kin yarda da ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China