Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wata sanarwa jiya Lahadi, inda ya yi kakkausar suka kan harin boma-bomai da aka kai wasu majami'u a biranen Tanta da Alexandria dake arewacin kasar Masar. Kwamitin sulhun ya jaddada cewa, ya zama dole a yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka kulla makarkashiyar kai harin, gami da wadanda suka ba da tallafi da wadanda suka kai harin. Ya kuma bukaci daukacin kasashen duniya da su ba da hadin-kai ga kasar Masar da sauran gwamnatocin kasashe a wannan fanni, bisa dokar kasa da kasa da ka'idojin MDD.
An kai wasu hare-haren bom kan majami'u a biranen Tanta da Alexandria dake arewacin kasar Masar a ranar 9 ga wata. Wata majiya daga ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta ce, hare-haren sun yi ajalin mutane a kalla 43, tare da raunata wasu sama da dari. Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren.(Murtala Zhang)