in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa sun bukaci Koriya ta Arewa da ta bi kudurin MDD
2017-09-16 13:26:38 cri
Da safiyar jiya Juma'a ne, Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami, wanda rahotanni daga Japan ke cewa, makamin ya wuce ta saman yankin arewacinta kafin ya fada tekun Pasifik.

Dangane da wannan lamari, kasashen Koriya ta Kudu da Rasha da Amurka da Sin, har ma da babban magatakardan MDD suka bayyana bacin ransu, inda suka yi kira ga Koriya ta Arewa, ta yi biyayya ga kudurin kwamitin sulhu na MDD tare da warware sabanin dake tsakaninta da bangarori daban- daban a siyasance.

Haka zalika, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa a jiyan, inda ya yi allah wadai da gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi, inda ya ce matakin ya bata ran gamayyar kasa da kasa.

Bugu da kari, bisa kiran da zaunannannun wakilan kasashen Amurka da Japan suka yi a jiya da yamma, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taron tattaunawa kan gwajin makamin na Koriya ta Arewa.

Bayan taron ne kuma aka fitar da wata sanarwa da ta yi Allah wadai da kakkausar harshe kan harba makamin, tana mai bukatar kasar ta dakatar da gwajin da take yi ba tare da bata lokaci ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China