in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya tattauna kan sabon gwajin nukiliyar Koriya ta arewa
2017-09-05 13:17:46 cri
A ranar 4 ga watan ne kwamitin sulhun MDD ya kara kiran taron gaggawa, kan sabon gwajin nukiliya da kasar Koriya ta arewa ta yi a ranar 3 ga wata.

A yayin taron, mataimakin babban sakataren MDD dake kula da harkokin siyasa Jeffrey Feltman ya ba da rahoto kan batun, ya kuma jaddada kakkausan zargin da babban sakatare Antonio Guterre ya yi, game da sabon gwajin makamin. Feltman ya jaddada cewa, babban sakatare na fatan ganin kwamitin sulhu ya ci gaba da hadin kai, tare kuma da daukar matakai masu dacewa.

A nasa bangare, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya nanata cewa, gwamnatin kasarsa na adawa da ta ga gwajin nukiliya da Koriya ta arewa ta yi, wanda ya saba wa kudurorin kwamitin sulhu. A waje guda kuma ya jaddada cewa, dole ne a warware matsalar zirin Koriya ta hanyar lumana, kana a kauracewa daukar matakan soja.

Kaza lika Liu ya bayyana cewa, alal hakika shawarar bai daya da kasashen Sin da Rasha suka gabatar, game da cimma burin raba zirin Koriya nukiliya a zirin, za kuma ta iya kawar da damuwar bangarori daban daban, da sassauta yanayin da ake ciki cikin sauri.

Taron dai wanda aka kira a ranar 4 ga wata, taro ne na gaggawa karo na biyu, wanda kwamitin sulhu ya kira a cikin mako guda, shi ne kuma taro karo na 10 game da batun Koriya ta arewa, wanda kwamitin sulhun ya kira a cikin shekarar nan ta bana. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China