in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DPRK ta sake harba wani makami mai linzami
2017-09-15 09:32:22 cri
Gwamnatin kasar Japan ta sanar a yau Jumma'a cewa, wani makami mai linzami da kasar Koriya ta arewa ta harba ya wuce ta saman arewacin kasarta kana ya fada tekun fasifik.

Mahukunatan na Japan su ka ce makamin ya sauka ne a nisan kilomita 2,000 gabas da yankin Erimo a Hokkaido da msalin karfe 7.16 na safe agogon Japan.

Harba wannan makami da Koriyar ta arewan ta yi, na zuwa ne bayan da kwamitin sulhun MDD ya kada kuri'ar amince da tsaurara wa kasar takunkumi, sakamakon gwaje-gwajen nukiliya a karo na shida da kasar ta yi a ranar 3 ga watan Satumba,.

Babban sakataren majalisar zartarwar kasar Japan Yoshihide Suga ya ce kasarsa ta yi allah wadai da kakkausar murya kan gwajin na baya-bayan, wanda ta bayyana a matsayin takalar fada.

Suga ya ce, makamin da Koriya ta arewan ta harba bai yiwa japan din wata illa ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China