in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da farautar wadanda ake tuhuma da aikata cin hanci
2017-03-08 20:10:30 cri

Yau Laraba ne kasar Sin ta sanar da kaddamar da shirinta na shekarar 2017 na farautar wadanda ake tuhuma da laifin cin hanci tare da maido da kudaden da suka sata daga kasashen ketare.

A shekarar 2016 ne kasar Sin ta dawo da mutane 1032 wadanda ake tuhumarsu da laifin cin hanci da karbar rashawa, kuma suka gudu zuwa kasashe da yankuna fiye da 70, ciki had da ma'aikatan gwamnati 134, da wasu 19 da ake nema ruwa a jallo, tare da maido da kudin Sin RMB biliyan 2.4 daga kasashen ketare wadanda suka sata. Yawan mutanen da kasar Sin ta kama da kuma kudaden da ta maido suna ta karuwa, lamarin da ya kara tsoratad da sauran mutanen da ake tuhumarsu da laifin cin hanci, da yanzu haka suka gudu zuwa ksashen waje. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China