Babban Jojin Sierra Leone Abdulai Hamid Charm, ya ce suna sane da muhimmancin cibiyoyin shari'a wajen inganta bada dama ga samun shari'a, amma kuma sun lura da iyakar da suke da ita.
Ya ce akwai bukatar masana harkokin shari'a, su hada hannu da cibiyoyin shari'a na al'umma domin bada dama ga wadanda ke matukar bukatar ayyukansu.
Abdulai Hamid Charm, na wannan jawabi ne yayin bude taron yini uku na nahiyar game da hadin gwiwa tsakanin bangaren shari'a da cibiyoyin shari'a na al'umma dake gudana a Kigali.
Taron ya samu mahalarta daga sama da kasashe 15 na fadin nahiyar, domin tattauna hanyoyin karfafa hadin gwiwa tsakanin bangaren shari'a da cibiyoyin shari'a na al'umma. (Fa'iza Mustapha)