in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bam da aka kaddamar a tsakiyar Somaliya ya halaka mutane biyu
2017-09-11 10:59:02 cri

Rahotanni daga kasar Somaliya na cewa, a kalla mutane biyu ne suka gamu da ajalinsu, kana wasu 15 kuma suka jikkata, ciki har da wasu 'yan jaridu uku, sanadiyar wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kaddamar a tsakiyar kasar.

Gwamnan yankin Hiiran Omar Adan Ibrahim ya tabbatar cewa, mutane biyu ne suka mutu maimakon uku da tun farko aka ba da rahoto, sai dai kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Adan Ibrahim ya ce, dan kunar bakin waken ya tarwatsa kansa a kusa da wani shahararren kanti da ke kusa da sansanin sojojin Djibouti dake yankin Hiiran. Haka kuma wasu 'yan jaridun Somaliya suna daga cikin wadanda suka jikkata, bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a kusa da wata cibiyar binciken ababan hawa dake garin Beledwayne.

Mai magana da yawun bangaren ayyukan sojojin Al-Shabaab Abdiasis Abu Musab ya ce, harin da aka kai a wajen ofishin gwamnan yankin Hiiran a lokacin da yake halartar wata ganawa, an shirya kaiwa jami'an gwamnatin yankin ne.

Mayakan Al-Shabaab wadanda ke kokarin kifar da gwamnatin Somaliya dake samun goyon bayan kasashen yamma, ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare, a daidai kokacin da yankin tsakiyar kasar ke fama da hare-haren ta'addanci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China