in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya amince zai jagoranci rajin yaki da rashawa na Afrika
2017-07-26 10:00:53 cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya amince zai jagoranci rajin yaki da rashawa na kungiyar tarayyar Afrika AU na shekarar 2018.

Sanarwar tace shugaba Buhari ya amince da sabon mukamin da aka bashi, kamar yadda ke kunshi cikin wasikar da ya aika ga takwaransa na kasar Guine Alpha Conde wanda kuma shi ne shugaban tarayyar Afirka a ranar 24 ga watan Yuli.

Shugaban Najeriyar yace ya gode da wannan matsayi da aka bashi, kuma ya jaddada aniyarsa na yin aiki tukuru da kuma bada gudunmowa wajen cigaban harkokin gwamnati da cigaban nahiyar Afrika baki daya.

A cikin sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, shugaba Buhari yace, zai yi aiki tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa domin cimma burin da aka sanya gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China