Za a yi muhawara kan wannan batu ne a ranar 8 ga watan nan a majalisar dokokin kasar.
Bayan rusa majalisar dokokin kasar a karshen Maris na bana da shugaba Zuma ya yi, jam'iyyar adawa ta kasar ta sake gabatar da batun yanke kauna ga salon mulkin shugaba Zuma, tana mai bukatar a jefa kuri'u ba tare bayyana rajistar masu kuri'ar ba, don sa kaimi ga 'yan majalisar dokokin kasar daga jam'iyyar dake kan karagar mulki, wadanda suke tsoron abun da ka je ya zo idan har suka jefa kuri'un amincewa.
Bisa dokokin kasar, idan aka zartas da kuri'ar debe kauna ga shugaba Zuma, shugaban da dukkan majalisar ministocin gwamnatinsa za su yi murabus, kana Mbete za ta zama shugabar kasar ta wucin gadi. (Zainab)