in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Zuma ya tsallake rijiya da baya a kuri'ar sirri da aka kada don tsige shi
2017-08-09 09:29:34 cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya a kuri'ar da aka kada don neman tsige shi a asirce.

Kakakin majalisar dokokin kasar Baleka Mbete, ya sanar da cewa 'yan majalisar 198 ne suka kada kuri'ar kin amincewa da kudurin tsige shugaban, yayin da 'yan majlisar 177 suka goyi bayan kudurin, 9 daga cikin 'yan majalisar kuma suka kauracewa kada kuri'ar.

'Yan majalisar dokokin na jam'iyyar ANC mai mulki sun kaure da shewa bayan da aka bayyana sakamakon.

Shugaban jam'iyyar Democractic Alliance Mmusi Maimane, ya bayyana cewa, za a cigaba da fafutukar tabbatar da ganin sun tumbuke Zuma daga mukaminsa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China