in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi tir da gwajin makamin nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi
2017-09-04 09:48:56 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da gwajin makami mai linzami ta karkashin kasa da Jamhuriyar Demokradiyyar Al'ummar Koriya ta sanar da aiwatarwa.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar jiya, Antonio Guterres ya jadadda kira ga shugabancin Koriya ta arewa da ya dakatar da yin gwaji tare da biyayya ga dokokin kasa da kasa karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD.

Ya ce wannan matakin sake sabawa dokokin kasa da kasa ne da kuma tarnaki ga yunkurin kasashen duniya na kawar da makamai. Inda ya bayyana gwajin a matsayin wanda ke barazana ga tsaron yankin.

Kakakin ya ce sakatare janar din zai ci gaba da tuntubar dukkan bangarorin da abun ya shafa.

A jiya Lahadi ne Jamhuriyar Demokradiyyar Al'ummar Koriya, DPRK ta yi gwajin makami mai linzami mafi karfi, tana mai ikirarin kirkirar bom mafi karfi mai sinadarin hydrogen da za a iya makalawa jikin linzamin da za a iya harbawa daga wata nahiya zuwa wata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China