UNCCD ya jinjinawa rawar da kasar Sin ke takawa a matakan yaki da kwararowar Hamada
Mataimakin sakataren babban taron yaki da kwararowar Hamada na MDD(UNCCD) Pradeep Monga, ya jinjinawa gagarumawar rawar da gwamnati da al'ummar Sinawa ke takawa, wanda ya kasance abin koyi a fannin yaki da kwararowar Hamada a duniya.
Jami'in ya bayyana hakan ne a hedkwatar UNCCD dake birnin Bonn na kasar Jamus,gabanin babban taron kan yaki da kwararowar Hamada karo na 13 da aka bude a yau Laraba a birnin Ordos,na yankin Mongolia ta gida dake nan kasar Sin.(Ibrahim)