in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron kara wa juna sani na kasa da kasa kan batun hadin kan Sin da kasashen Afirka da ci gaban Afirka a Malawi
2017-09-11 14:16:54 cri

A kwanan baya ne a Lilongwe, babban birnin kasar Malawi, aka shirya taron kara wa juna sani na kasa da kasa game da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da kuma ci gaban Afirka a karkashin jagorancin ofishin kasar Sin dake Malawi, da ma'aikatar harkokin waje da hadin kai da kasa da kasa ta kasar Malawi. Masana da suka fito daga kasashe 11 na Afirka da na kasar Sin sun tattauna sosai kan yadda kanana da matsakaitan kasashe dake nahiyar Afirka suke samun ci gaba ta hanyar hadin kan Sin da Afirka.

Kasar Malawi dake kudancin Afirka, karamar kasa ce kana matsakaiciya ko a fannin fadin kasa ko kuma a fannin yawan al'umma. Wani malamin jami'ar nazarin albarkatun halittu ta Lilongwe Matthews Mkandawir yana ganin cewa, kafuwar dangantakar abokantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da kasashen Afirka, da gabatar da shawarar 'Ziri daya da hanya daya' sun samar da dama mai kyau ga kasashen Afirka kanana da matsakaita, ciki har da Malawi wajen samun bunkasuwa, amma duk da haka akwai bukatar jama'ar Malawi su kara yin amfani da wannan dama da kasar Sin ke samar musu, don haka ya ba da shawarar cewa, kamata ya yi Sin da kasashen Afirka su kara yin cudanya.

'Akwai gibi tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin yin cudanya. Yawancin Sinawa ba su fahimci nahiyar Afirka ba, ciki har da Malawi, a sa'i guda kuma jama'ar Malawi ba su fahimci kasar Sin. Don haka, kamata ya yi mu kafa wasu hukumomi, kamar cibiyar bayanan kasar Sin a kasar Malawi, hakan zai taimaka wajen samar da muhimman bayanai game da kasar Sin.'

A jawabinsa,wani masani daga jami'ar kasa ta Lesotho Moh ya bayyani dalla-dalla game da yadda yake kallon fasahohin da kasar Sin ta samu wajen samun ci gaba, ciki har da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, jawo jarin waje, da kuma gina yankin musamman da aka ware don samun ci gaba da dai sauransu. Yana mai cewa, kasashen Afirka suna iya koyon abubuwa da dama daga wadannan fasahohi.

'Ya kamata gwamnatocin kasashen Afirka su yi koyi da kasar Sin, kamar samar da yanayin da ya dace ga masu sha'awar zuba jari, kana da kara zuba jari ga bangaren ba da ilmi da horar da kwararru, baya ga haka, su koyi fasahohin zamani, hakan zai taimakawa kasashen nahiyar cin gajiyar albarkatun da Allah ya hore musu yadda ya kamata, tare kuma da tabbatar da samun ci gaba.'

Shugaban sashen nazarin ci gaban shiyya-shiyya na cibiyar nazarin kudancin Afirka da adana muhimman bayanai ta kasar Zimbabwe Joseph Ngwawilomi James Mahlelebe yana ganin cewa, aikin gona wata muhimmiyar sana'a ce ga kanana da matsakaitan kasashen Afirka da dama, don haka bunkasuwar wadannan kasashe sun dogaro ne da ci gaban aikin gona. Ya ce, yana fatan a nan gaba kasar Sin za ta kara yada fasahohinta na aikin gona tare da zuba jari a fannin aikin gona a kasashen Afirka.

'Kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara, ban da kasar Afirka ta kudu dukkansu ba su samu isassun jari da ake bukata a bangaren aikin gona na zamani ba, ban da wannan kuma akwai tsada wajen shigar da injuna daga kasashen waje, muna fatan kasar Sin za ta kara yada fasahohinta na aikin gona a kasashen Afirka, kamar yadda ta kafa cibiyar nuna fasahohin aikin gona a Afirka, kana muna fatan Sin za ta kara zuba jari a fannin amfani da na'urorin aikin gona, don rage kudaden da kasashen Afirka ke kashewa a wannan fannin.'

Jakadan kasar Zambia dake Malawi John Jafete Ngwata Phiri a cikin jawabinsa ya waiwayi wasu muhimman taimako da kasar Sin ta bai wa kasarsa tun bayan kasar ta samu 'yancin kai. A cewarsa, 'idan babu kasar Sin, ban san yaya kasar Zambia za ta kasance a yanzu ba'.

'Ya kamata mu yi koyi daga jama'ar kasar Sin, ba su da son kai, suna da kwazo kana suna da da'a, wadannan su ne abubuwa da suka cancanta mu yi koyi da su, su ne kuma muhimman abubuwa da za su taimaka mana wajen kawar da talauci da tabbatar da samun ci gaba.'

A yayin wannan taron kara wa juna sani, masana da masu masana'antu sama da 20 da suka fito daga kasar Sin da kasashen Afirka ne suka tattauna sosai kan hadin kai a tsakanin bangarorin biyu a karni na 21, da yadda jama'ar kasashen Afirka kanana da matsakaita za su ci gajiya ta hanyar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, da za a kalli abubuwan da kasashen Afirka suka samu wajen samun bunkasuwa daga fasahohin da Sin ta yi amfani da su, da kuma kalubalen da kasashen Afirka ke fuskanta wajen samun bunkasuwa da hanyoyin da za a bi wajen tinkarar su. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China