in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin ruwa ba da tallafin kiwon lafiya na sojojin ruwan kasar Sin ya taimakawa jama'ar kasar Djibouti
2017-08-28 12:58:28 cri

A ranar 26 ga wata ne, jirgin ruwan ba da kiwon lafiya na sojojin ruwan kasar Sin mai suna "Peace Ark" dake gudanar da aiki a kasar Djibouti ya karbi marasa lafiya masu yawa, kuma jama'ar kasar sun nuna maraba kwarai da zuwansa, a wannan rana ya bada jinya ga mutane kimanin dubu daya. Sai dai wannan jirgin ruwan ya sake zuwa kasar Djibouti ne bayan shekaru 7 da suka gabata.

Jirgin ruwan ba da jinya na Peace Ark ya isa kasar Djibouti dake yammacin gabar mashigin tekun Aden a arewa maso gabashin nahiyar Afirka, inda ya fara kai ziyara tare da samar da hidimar bada jinya har na tsawon kwanaki 9 a kasar. A kwanakin da suka wuce a jere, jama'ar kasar Djibouti da dama sun ziyarci jirgin ruwan har suka ga likitoci. A safiyar ranar 26 ga wata, mutane da dama ne suka yi dogon layi suna jiran ganin likitoci. Solomon Adsedha mai shekaru 39 da haihuwa ya gamu da matsalar koda, ya kuma yaba da kulawar da likitan sojojin ruwan kasar Sin ya ba shi. Ya ce,

"Na sha magani, an yi min bincike a koda ta. Na kawo takardun bincike da na taba yi a wasu wurare, ina son likitan Sin ya duba su. Zan je a dauki hoton sassan jiki na musamman a nan, akwai na'urori masu inganci a nan, ina fatan za su ci gaba da zuwa nan, na gamsu sosai da hidimarsu."

Jirgin ruwan "Peace Ark" ya taba kawo ziyara kasar Djibouti a shekarar 2010 inda ya samar da hidimar bada jinya kyauta, wanda ya samu maraba sosai daga jama'ar kasar. A wannan karo, jirgin ruwan ya sake kawo ziyara kasar, ban da bada jinya a cikin jirgin ruwan, an kuma tura masana zuwa asibitocin bangaren soja da horar da likitoci dake wurin, an kuma tura rukunonin likitoci zuwa kauyuka don kula da marasa lafiya.

Mutane da dama sun shafe tsakar ranar 26 ga wata suna jiran ganin masana lafiya na jirgin ruwan "Peace Ark" ya tura zuwa asibitin bangaren soja mai kula da mata da kanana yara na kasar Djibouti. Likita Zhang Zhiyong ya bada jinya a asibitin har na tsawon kwanaki biyu, wannan ne karo na uku da ya gudanar da irin wannan aiki tare da jirgin ruwan "Peace Ark". Zhang Zhiyong ya bayyana cewa,

"Tun da safe suke jiran mu, mu zo nan da karfe 8, sun shiga layi suna jira tun daga karfe 6 da safe. Iyalan sojoji su ma sun zo, akwai mata da kananan yara da tsofaffi da kuma maza. Likitocin dake wurin suna begen zuwanmu, wannan shi ne karo na farko da muka zo nan, sun ce za su yi aiki tare da mu har zuwa lokacin da za mu kammala aikin mu a nan.

Da tsakar rana, mazaunan wani kauyen dake wajen birnin Djibouti sun zo wani aji dake wata makarantar wurin, inda likitocin jirgin ruwan na Peace Ark dake kula da marasa marasa lafiya suka duba su, wasu kananan yara sun yi rawa don maraba da zuwan likitocin Sin. Wani mutum mai suna Yusuf wanda mai shekaru 27 da haihuwa ya bayyana bayan da ya saurari binciken da likitan Sin ya yi masa cewa,

"Wannan ne karo na farko da suka zo nan, za su yi kwanaki biyu a nan. Wannan tawagar likitoci tana da kyau, suna da kwarewa sosai."

Jirgin ruwan Peace Ark wani dandalin bada jinya a kan teku da kasar Sin ta kafa da kanta, wanda yake da dakunan gudanar da aikin tiyata 8, da cibiyoyin nas-nas 8, da dakunan binciken cututtuka 18, da kuma gadaje 300. Likitoci 115 daga asibitocin sojojin ruwan kasar Sin ne suka shiga aikin a wannan karo, bayan kasar Djibouti, za kuma su tafi zuwa kasashen Saliyo, Gabon, Jamhuriyyar Congo, Angola, Mozambique, Tanzania, da kuma Timor ta gabas don kai ziyara da samar da hidimar bada jinya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China