in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron kawar da talauci da neman ci gaba na FOCAC a Mauritius
2017-09-07 11:20:28 cri
A jiya Laraba ne aka bude taron tattaunawa game da kawar da talauci da neman ci gaba na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da nahiyar Afirka na FOCAC a birnin Balaclava na kasar Mauritius.

Yayin taron, jami'ai da masana daga kasashen Sin da Afirka 12 sun tattauna game da yadda Sin da Afirka za su fuskanci kalubalolin kawar da talauci cikin hadin gwiwa, domin neman hanyoyi masu amfani, wadanda za su inganta hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a wannan fanni.

Wakilin tawaga mai ba da jagoranci kan raya harkokin kawar da talauci ta majalisar gudanarwar kasar Sin Xia Gengsheng, ya ba da jawabi a yayin taron, inda ya bayyana cewa, ana sa ran fitar da dabaru masu kyau, wadanda za su ba da taimako wajen kawar da talauci a kasashen Sin da Afirka.

Ya ce, ya dace a hada manyan shirye-shiryen hadin gwiwar Sin da Afirka guda goma, da jadawalin kudurorin ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2063 na kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU tare, domin nuna goyon baya ga kasashen Afirka don raya tattalin arzikinsu, da kuma samar da karin guraben ayyukan yi a kasashen, ta yadda za a kawar da talaucin.

Hakan a cewar sa, zai ba da gudummawa wajen neman bunkasuwar kasashen Afirka, da kuma tallafawa al'ummomin kasashen Sin da Afirka yadda ya kamata.

An yi taron kawar da talauci da neman ci gaba na Sin da Afirka karo na farko a shekarar 2010, domin karfafa mu'amala tsakanin Sin da Afirka bisa wannan fanni. Sa'an nan, an shigar da taron cikin jadawalin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a hukunce a shekarar 2015. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China