A cikin wasikar, ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta bayyana cewa, tun da aka kafa wannan kawance zuwa wannan lokaci, ta kai hare-hare ta sama sau da dama. Ta ce, koda a watan Yulin bana, kawancen ya kai hare-hare ta sama sau 7 a jihar Deir ez-Zor dake gabashin kasar Syria da jihar Al Hasakah dake arewa maso gabashin kasar, wadanda suka haddasa mutuwa da raunatar fararen hula da dama, ciki har da mata da yara.
A watan Satumba na shekarar 2014 ma, kawancen kasa da kasa wanda kasar Amurka da sauran kasashe suka kafa ya kai hare-hare ta sama kan sansanonin kungiyar IS dake kasashen Syria da Iraki. A saboda haka gwamnatin kasar Syria na ganin cewa, kawancen da Amurkar ke jagoranta bai samu izinin kai irin wadannan hare-hare daga kwamitin sulhun MDD ba, wadanda suka haddasa mutuwa da raunatar fararen hula da dama. (Zainab)