in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Tattaunawa da takunkumi su ne hanyoyin warware matsalar zirin Koriya
2017-09-07 19:26:31 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, hanya daya tilo ta kawo karshen batun Zirin Koriya, ita ce sanya takunkumi da kuma tattaunawa mai ma'ana.

Wang ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ko kadan ba ta goyon bayan gwajin makami mai linzami da kasar Koriya ta arewa ta yi, matakin da ya ce ya sabawa kudurori kwamitin sulhu na MDD. Jami'in na kasar Sin ya ce kasarsa tana goyon bayan karin matakan da kwamitin sulhun MDD ke dauka game da wannan batu. A don haka ya yi kira ga kasashen duniya, da su yi yunkurin ganin an koma kan teburin sulhu, tare da fatan mambobin kwamitin sullhun na MDD za su hada kansu don cimma matsaya guda ta hanyar aikewa da sako mai karfi game da wannan matsala.

Ya ce sanya takunkumi wani muhimmin bangare na kawo karshe matsalar nukiliyar zirin Koriya, baya ga batun tattaunawa mai ma'ana.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China