Cikin wata sanarwa da ta fitar, MDD tace a kalla yara miliyan 48 da matsalolin suka fi shafa ne ake saran zasu ci gajiyar wannan shirin bada agajin gaggawar na hukumar ta UNICEF a shekarar nan ta 2017, wanda aka kaddamar daga ranar 31 ga watan Janairun wannan shekara.
An yi kiyasin daya daga cikin hudu na yaran duniya suna rayuwa a kasashen da rikici ko bala'u suka shafa.
UNICEF ta bayyana fargabar cewa yara kusan miliyan 7.5 ne zasu iya fuskantar matsalar matukar karancin abinci mai gina jiki a kasashen duniya da matsalar ta shafa, kuma kananan yara kusan rabin miliyan ne suna arewa maso gabashin Najeriya da kasar Yemen.
Sai dai har yanzu akwai sarkakiya, sakamakon rashin tantance alkaluma a yankin tafkin Chadi saboda rashin samun damar shiga yankin sakamakon fargabar hare haren mayakan Boko Haram. Sashen bada agajin jin kai na hukumar ta UNICEF ya kaddamar da gidauniyar neman taimakon ne na 2017, domin gudanar da muhimman ayyuka da suka shafi tallafawa kananan yara da ruwan sha mai tsabta, abinci mai gina jiki, ilmi, kiwon lafiya, da kuma baiwa yaran kariya daga barazanar hare hare a kasashen da matsalar tafi kamari.