in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD ya jawo hankalin kalubalen kare yara daga yaki
2015-06-09 09:28:13 cri

Kasashe mambobin MDD a ranar Litinin din nan suka samu rahoton magatakarda Ban Ki-moon wanda ya gabatar game da yara da tashin hankali na makamai, inda a ciki ya jawo hankalin kalubalen da ba'a iya kaucewa ba a shekarar bara wajen kare miliyoyin yara da girma a kasashen da ake yaki da makamai.

A cikin rahoton shi na baya bayan nan, magatakardar majalissar ya mai da hankali ne a kan yanayin da duniya ke fuskanta a yanzu dangane da tashin hankali da makamai a kan yara a kalandar bara na 2014.

Rahoton da magatakardar kan gabatar wa kwamitin tsaro na majalissar sau daya duk shekara ya bayyana cewa, a hakikanin gaskiya hakan yake a yawancin wuraren da ake fuskantar tashin hankali, musamman a kasashen kamar su jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Iraqi, Isra'ila, Palestinu, Nigeriya, Sudan ta Kudu, da kuma Syria wadanda suka fuskanci tsananin tashin hankali.

Cin zarafin yara yanzu haka yana ci gaba da faruwa a fadan da ake kan yi kamar a Afganistan, jamhuriyar demokradiya ta Kongo da kuma Somaliya, in ji rahoton.

Na baya bayan nan yanayin tsaro a Yemen ya yi muni, inda rahoton da aka samu a watan Afrilu kadai na wannan shekarar ya nuna karin adadin yara da suka rasa rayukansu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China