Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ya ce, wadannan jagorori sun hada da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim,babbar darektar asusun ba da lamuni na kasa da kasa Christine Lagarde, da babban darektan kungiyar cinikayya ta duniya Roberto Azevedo, da babban darektan kungiyar kwadago ta duniya Guy Ryder. Sauran sun hada da babban sakataren kungiyar tattalin arziki da raya kasashe Angel Gurria sai kuma shugaban hukumar daidaita harkokin kudi Mark Carney.(Ibrahim)