An bude taron kasashen da suka kulla yarjejeniyar tinkarar kwararowar hamada ta MDD karo na 13 a birnin Ordos dake arewacin kasar Sin. Mutane fiye da 2000, da suka zo daga kasashe 196 da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 20 ne ake saran za su halarci taron da za a kwashe makonni 2 ana gudanar da shi.
Babban taken taron shi ne " hada hannu don tinkarar kwararowar hamada, ta yadda za a tabbatar da kare muradun daukacin bil Adam".(Bello Wang)