A jawabinsa yayin liyafar, shugaban kungiyar Yang Faming ya bayyana cewa, a madadin wakilan kungiyar, yana taya daukacin Musulmai na kasar Sin, da sauran kasashen duniya murnar babbar salla, kana yana fatan alheri da dauwamammen ci gaban kasar Sin, da kuma zaman lafiya a duniya baki daya.
Jakadu sama da 40 wadanda suka zo daga kasashe masu bin addinin Musulunci, da wakilan musulmai na kasashen ketare wadanda suke zaune a birnin Beijing, da wasu jami'an gwamnatin kasar Sin, da kuma wakilan Sinawa masu bin addinin Musulunci, gaba daya kimanin mutane dari 3 sun halarci wannan bikin liyafa. (Maryam)