in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kasar Sin ya bukaci mawallafa su kara kaimi
2017-08-25 12:12:35 cri

Babban jami'in kasar Sin Liu Yunshan, ya bukaci marubuta da su kara kaimi game da al'adun kasar Sin da kuma daga martabar kasar ta yadda za ta zama mai karfin fada a ji ta fuskar masana'antun dab'i.

Liu, wanda mamba ne a kwamitin tsakiya mai kula da al'amuran siyasa na jam'iyyar kwamitin ta kasar Sin (CPC), ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya ziyarci bikin baje kolin littattafai na kasa da kasa na Beijing karo na 24.

Mista Liu ya ce, ya kamata mawallafa su mayar da hankali wajen inganta rubutunsu, kuma su kara azama wajen isar da sakwanni na kasa da kasa domin samun gagarumin cigaban masana'antun dab'i.

Bikin baje kolin littattafan wanda aka shirya gudanarwa tsakanin ranar 23 zuwa 27 ga watan Augasta, ya samu halartar 'yan kasuwa kimanin 2,511 daga ciki da wajen kasar Sin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China