in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru: Tsarin tattaunawa tsakanin kasashen BRICS da sauran kasashe masu tasowa zai inganta hadin kan da ake gudanar yanzu haka
2017-09-06 11:01:47 cri

A safiyar jiya Talata ne aka gudanar da taron tattaunawa tsakanin kasashe da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa, a cibiyar taron kasa da kasa dake birnin Xia'men na kasar Sin, inda shugabannin kasashe mambobin BRICS suka tattauna tare da shugabannin wasu kasashe masu tasowa, ciki har da Masar, Mexico, Tajikstan, Guinee da Thailand da dai sauransu. Game da irin yadda tattaunawar ta gudana kwararru sun bayyana ra'ayoyinsu.

Kwararru suna ganin cewa, ban da hadin kai a tsakaninsu, kamata ya yi kasashen BRICS su yi tattaunawa tare da sauran kasashe masu tasowa, don kara bayyana wa duniya ra'ayoyin kasashen da tattalin arzikinsu ke samun saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa. Haka kuma irin wannan tsarin tattaunawar zai iya zurfafa hadin kai a tsakanin dukkanin kasashe masu tasowa a duniya.

Mataimakin shugaban sashen nazarin harkokin kasuwanci, na kwalejin nazarin hadin kan cinikayya da tattalin arziki a ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, mista Bai Ming ya bayyana cewa, a matsayinsa na muhimmin aiki musamman a yayin taron shugabannin kasashen BRICS, wannan taron tattaunawar ya bayyana sosai hanyoyi biyu da ake bi wajen samun bunkasuwar tsarin kasashen BRICS, wato inganta hadin kai a tsakanin kasashen biyar na BRICS, da bunkasa dangantakar dake tsakaninsu da sauran kasashe masu tasowa. Sai dai a ciyar da hanyoyin biyu gaba baki daya, za a iya kara bayyana ra'ayoyin kasashen BRICS, da na sauran kasashe masu tasowa a harkokin duniya.

"Tsarin hadin kai na kasashen BRICS, wani tsarin hadin kai ne mai fadada, kasashe biyar na kungiyar BRICS na aiki kafada da kafada wajen daukar matsayin bai daya domin daidaita sahu da kasashe masu wadata, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, kasashen BRICS su bayyana ra'ayoyin kasashe masu tasowa a duniya. A ganina, ci gaban kasashen BRICS na hade da fannoni guda biyu, wato kara yawan mambobin kasashen BRICS yadda ya kamata, da kuma kara tattaunawa tare da sauran kasashe masu tasowa. Ta haka za a iya kara samun ikon bayyana ra'ayoyi, musamman irin na wakilci."

A nasa bangare, daraktan cibiyar hadin kan kasashen BRICS, na jami'ar koyar da malamai ta Beijing, mista Wang Lei ya bayyana cewa, an kafa tsarin hadin kai na kasashen BRICS ne, don wakiltar kasashe da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa. Don haka tabbas tsarin na samun ci gaba a yadda yake a yanzu haka.

"Irin tsarin hadin kai a tsakanin kasashen BRICS da kasashe masu tasowa, ya nuna matsayin da kasashen BRICS ke dauka, na wakiltar moriyar bai daya ta dukkanin kasashe masu tasowa. A hakika dai, tsarin ya hade da wasu manyan kasashe da tattalin arzikinsu ke samun saurin bunkasuwa, musamman irin kananan kasashe da ba su da damar zama kasashe masu wadata a cikin tsarin hadin kai na kasashen BRICS."

A yayin taron tattaunawar din tsakanin kasashe da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasa da kasashe masu tasowa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya nuna cewa, shawarar 'Ziri daya da hanya daya' da Sin ta gabatar tana dacewa da ajandar neman dauwamammen ci gaba kafin shekarar 2030 na MDD. Mista Bai Ming yana mai cewa, kasashen BRICS za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da shawarar. A cewarsa, yawancin kasashen da shawarar 'Ziri daya da hanya daya' ke shafar su ne kasashe masu tasowa, a karkashin jagorancin kasashen BRICS, da kuma hada kan shawarar 'Ziri daya da hanya daya' da ajandar bunkasuwa kafin 2030, ba shakka duk kasashe masu tasowa za su iya cin gajiya daga wajen irin tsarin hadin kai.

"A hakika dai, ba kasar Sin ce kadai ba ke gudanar da wannan aiki na raya 'Ziri daya da hanya daya'. Kasar Sin ta gabatar da shawarar ce kawai, kuma sauran kasashe sun amsa cikin himman da kwazo. A yayin da ake kokarin tabbatar da shawarar, ya kamata kasashen BRICS su taka muhimmiyar rawa. Ta tsarin hadin kai, za su iya wakiltar kasashe masu tasowa, don kara baiwa kasashen damar samun ci gaba, a yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya. Kana a kara samun daidaito kan dangantakar dake tsakaninsu da kasashe masu ci gaba." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China