in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS a birnin Xiamen
2017-09-05 19:56:32 cri

Yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da manema labarai na gida da na kasashen waje a cibiyar taron kasa da kasa ta birnin Xiamen, inda ya yi bayani kan taron shugabannin kasashen BRICS karo na 9 da taron tattaunawa tsakanin kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa.

Babban taken taron shugabannin kasashen BRICS na wannan karo shi ne karfafa dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen BRICS, a kokarin samar da wata makoma mai haske. A tsawon taron ganawar, shugabannin kasashen biyar sun yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a inganta hadin gwiwa da kara yin mu'amalar al'adu a tsakaninsu, da kokarin bullo da tsare-tsare, gami da sa hannu cikin ayyukan daidaita matsalolin tattalin arzikin duniya. Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da manema labarai na gida da na waje, ya bayyana cewa, shugabannin sun kuma cimma matsaya daya kan wadannan batutuwa da suka tattauna a kai, kana sun zartas da "sanarwar shugabannin kasashen BRICS ta Xiamen". Xi ya kara da cewa,

"An zartas da "sanarwar shugabannin kasashen BRICS ta Xiamen", inda aka sake jaddada tsarin BRICS na gudanar da hadin gwiwa ta moriyar juna ba tare da rufa rufa ba, da sakamakon da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata, da kuma fito da wani sabon shiri game da karfafa huldar abokantaka dake tsakanin kasashen BRICS. Shugabannin kasashen sun bayyana aniyyar cewa, za su hada kai matuka tare domin kara zurfafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a cikin shekaru goma masu zuwa."

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, yanzu shekaru fiye da goma ke nan da yin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, ya kamata a rika kyautata tsarin BRICS ta yadda zai dace da zamanin da muke ciki, tare da tabbatar da ci gaban hadin gwiwar kasashen. Kafin wannan taro, kasashen BRICS sun gudanar da taruka tsakanin wakilansu masu kula da harkar tsaro, da kuma ministocin harkokin wajensu, ban da haka kuma, kasashen 5 sun bullo da wani tsari na musayar ra'ayi tsakanin zaunannun wakilansu dake MDD. Dangane da batun daidaita tsarin kungiyar BRICS, Xi Jinping ya kara da cewa,

"Dukkanmu muna goyon bayan matakin karfafa iko na jami'in gudanarwa, da aiwatar da manufofin da muka tsara a baya, da kokarin neman sabuwar hanyar hadin gwiwa. A shekarar da muke ciki, an samu ci gaba sosai ta fuskar kyautata tsarin kungiyar BRICS, inda muka gabatar da tawagar jami'ai masu kula da cinikayya ta yanar gizo, da hadaddiyar kungiyar dakunan adana kayayyakin tarihi, da kungiyar dakunan karatu, da dai makamantansu. Wadannan tsare-tsare za su taimakawa kokarinmu na zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninmu a fannonin siyasa, tattalin arziki da al'adu."

Abin da kasashen BRICS ke gudanarwa shi ne shawarwari da hadin gwiwa a tsakanin kasashen kungiyar da kuma kasashen da tattalin arzikinsu ke samun saurin bunkasuwa da kasashe masu tasowa. Lamarin da ya sha bamban da lokutan baya shi ne kasar Sin ta gayyaci wakilan kasashe na yankuna daban daban na duniya a wannan karo. A ganin shugaba Xi Jinping, wakilan kasashen da tattalin arzikinsu ke samun saurin bunkasuwa da na kasashe masu tasowa sun bayyana aniyyarsu ta zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa ta yadda za a samu bunkasuwa a duniya ta hanyar hadin gwiwa. Xi Jinping ya bayyana cewa,

"Shugabanni mahalartar shawarwarin na ganin cewa, kamata ya yi kasashen da tattalin arzikinsu ke samun saurin bunkasuwa da kasashe masu tasowa su kara taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030, da kyautata tsarin daidaita tattalin arzikin duniya. Ban da wannan kuma, ya kamata a zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, da bullo da tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da sauran kasashe, a kokarin samun bunkasuwa mai dorewa ta hanyar kirkire-kirkire da samun daidaito da bude kofa da kiyaye muhallin halittu, da amfanawa kowa, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya da samun ci gaban kasa da kasa tare."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China