in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ware dala miliyan 500 domin bunkasa hadin gwiwar fasahohi tsakanin kasashen BRICS
2017-09-04 13:45:25 cri
Kasar Sin za ta ware zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan 500, domin tallafawa shirin bunkasa hadin gwiwa a fannin ci gaban fasahohi na kungiyar BRICS.

Shugaba Xi Jinping na kasar ta Sin ne ya bayyana hakan, cikin jawabinsa yayin taron shugabannin kungiyar na tara, wanda ya gudana yau Litinin a birnin Xiamen dake lardin Fujian na nan kasar Sin.

Ya ce baya ga batun fasahohi, za a yi amfani da kudaden wajen bunkasa sassan da suka shafi tattalin arziki, da cinikayya da zuba jari, da sauran fannoni na cinikayya na hada hadar kudade. Sauran bangarorin sun kunshi samar da ci gaba mai dorewa, da kirkire kirkire, da hadin gwiwar bunkasa masana'antu.

Daga nan sai ya bukaci kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, da su kara azama wajen aiwatar da manufofin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba, tare da watsi da manufofin sanyawa kasuwanni shinge.

Shugaba Xi ya ce duba da irin sauye sauye da duniya ke fuskanta, hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar BRICS na kara zama mai matukar muhimmanci. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China