in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi jinping ya ba da jawabi a yayin taron dandalin harkar masana'antu da cinikayya na kasashen BRICS
2017-09-03 17:54:17 cri

Da yammacin yau agogon kasar Sin ne aka bude taron dandalin harkar masana'antu da cinikayya na kasashen BRICS a birnin Xiamen, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai lakabi "A kokarta don inganta hadin kan kasashen BRICS cikin shekaru goma masu zuwa". Cikin jawabin kuwa, Shugaba Xi ya jaddada cewa, hadin gwiwar kasashen BRICS na cikin wani muhimmin lokaci, wadanda ke fuskantar muhimman ayyukan da suka kunshi raya tattalin arziki da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Ya ce ya kamata kasashen su kiyaye manufar hadin kan tattalin arziki, su kuma aiwatar da tsare-tsaren hadin gwiwa na kungiyar, tare da sa kaimi ga inganta tsarin hadin gwiwarsu daga dukkan fannoni.

Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 20 da kafuwar tsarin hadin kan kasashen BRICS, don haka taron dandalin harkar masana'antu da cinikayya na kasashen BRICS na bana ya jawo hankalin mutane sosai. A cikin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, kasashen BRICS sun yi namijin kokari wajen neman bunkasuwa tare, sa'an nan sun inganta hadin gwiwar su don moriyar juna, baya ga sauke nauyi da ke wuyansu don ba da gudummowarsu ga fadin duniya. Ya kara da cewa,

"Mu kasashe biyar, mu taimakawa juna da kara yin mu'amala da juna, da kafa tsarin hadin gwiwa a dukkan fannoni da shugabannin kasashen suke jagoranta, da gudanar da wasu ayyukan hadin gwiwa da suka dace da tsare-tsaren kasashen biyar da moriyar jama'ar kasa da kasa. Musamman kafa sabon bankin raya kasa da shirin ajiye kudi domin bukatun gaggawa da samar da gudummawa a fannin tattara kudi ga kasashen BRICS a fannonin gina ayyukan more rayuwa da samun bunkasuwa mai dorewa, da kyautata tsarin sarrafa tattalin arzikin duniya da kiyaye tsaron hada-hadar kudi na duniya."

Ban da wannan kuma, shugaba Xi ya nuna cewa, nuna daidaito ga juna, da cimma ra'ayi daya tare da mai da hankali kan kirkire-kirkire da cin moriyar juna ta hanyar hadin gwiwa, da kuma raya kai da yanayin duniya baki daya, manufofi ne da kasashen BRICS suka bi a cikin shekaru goma da suka gabata, wadanda ya kamata a ci gaba da bin su a nan gaba. Yanzu hadin kan kasashen na cikin wani muhimmin lokaci, la'akari da yadda tsarin tattalin arzikin duniya ke sauyawa, da kuma yadda cigaban kasashen BRICS ke tafiyar hawainiya, to ta yaya za a warware wannan matsala? Game da wannan, Shugaba Xi ya gabatar da shawarwari inda ya ce,

"Kar a mai da hankali kan saurin cigaban tattalin arziki kawai, maimakon haka, ya kamata a yi hangen nesa, da daidaita tsarin tattalin arziki, don neman sabbin damammaki da dabarun raya tattalin arziki. Kamata ya yi a yi amfani da damar dake tare da ci gaban fasahohin masana'antun duniya, don kirkiro sabbin fasahohi, da neman karuwar tattalin arziki, da sauyawar tsarinsa, da kokarin shiga a dama da mu a wani yanayi na samar da sabbin damammaki da suka hada da bangarorin masana'antu, da yanar gizo na Internet, da tsarin tattalin arziki mai amfanawa kowa. Ya kamata a yi kokarin gyara tsohon tsarin tattalin arziki, don kau da shingen dake hana ci gabansa, da samar da wani nagartaccen yanayi ga kasuwanni da al'ummomi, ta yadda za a samu ci gaba mai inganci da dorewa."

Haka zakila, shugaba Xi ya jaddada cewa, hadin gwiwar tattalin arziki tushe ne na tsarin kungiyar kasashen BRICS, kuma ya kamata kasashen su kiyaye wannan manufa, su kuma aiwatar da tsare-tsaren hadin gwiwa na kungiyar, tare da sa kaimi ga inganta tsarin hadin gwiwarsu daga dukkan fannoni. Baya haka kuma ya kamata kasashen su ba da gudunmuwarsu wajen kyautata harkokin tattalin arzikin duniya. Shugaba Xi yana mai cewa,

"Kasashen da suka fi samun saurin ci gaban tattalin arziki da kuma kasashe masu tasowa suna kokarin kara raya tattalin arzikin duniya ne domin ciyar da kansu gaba, a maimakon kwace moriyar wasu. Dole ne kasashen BRICS su hada kansu domin jagorantar dinkewar tattalin arzikin duniya da samar da karin sabbin tunani da hidimomin al'umma, da kara azama kan kafa salo da ka'ida ta fuskar tafiyar da ayyuka domin kowa ya ci gajiya, da sa kaimi kan sake kafa tsarin rarraba ayyuka a duniya da kyautata tsarin kamfanonin kasa da kasa. Ban da haka kuma, dole ne kasashen BRICS su kara azama kan yin gyare-gyare kan tsarin tafiyar da ayyukan kasa da kasa, wanda zai bayyana halin da muke ciki a fannin tattalin arzikin duniya a yanzu. Har ila yau wajibi ne a kyautata ka'idojin tafiyar da ayyukan da suka shafi teku mai zurfi, yankuna masu tarin kankara, sararin samaniya, yanar gizo ta Internet, a kokarin ganin kasashen duniya suna cin gajiya cikin adalci, tare da sauke nauyi tare. "(Kande/Zainab/Bello/Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China