in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron shugabannin kasashen BRICS da za a yi a Xiamen zai bude sabon shafi ga tsarin kungiyar
2017-08-29 10:48:47 cri

A watan Satumban dake tafe ne, shugabannin kasashen wakilan kungiyar BRICS za su yi ganawa karo na 9 a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin, yayin taron share fagen da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya a jiya Litinin da safe, kwararrun dake aiki a cibiyar cudanyar tattalin arzikin kasa da kasa ta kasar Sin da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin sun yi nuni da cewa, ganawar za ta bude wani sabon shafi ga tsarin hadin gwiwa na kungiyar a cikin shekaru goma masu zuwa.

Kawo yanzu, shekaru goma ke nan da kafa tsarin hadin gwiwa na kungiyar kasashen BRICS, alkaluma na nuna cewa, adadin tattalin arzikin kasashe biyar na BRICS ya karu daga kaso 12 bisa dari kafin shekaru goma zuwa kaso 23 bisa dari a yanzu, daga cikin adadin tattalin arzikin duniya, adadin cinikin duniya na kungiyar shi ma ya karu daga kaso 11 bisa dari zuwa kaso 16 bisa dari, kana adadin jarin da kasashen suka zuba a kasashen waje shi ma ya karu daga kaso 7 bisa dari zuwa kaso 12 bisa dari. Wannan yana nuna cewa, kasashen BRICS suna taka muhimmiyar rawa wajen karuwar tattalin arziki a fadin duniya.

Kwararren dake aiki a cibiyar cudanyar tattalin arzikin duniya ta kasar Sin Zhang Yansheng yana ganin cewa, a cikin shekaru goma masu zuwa, wadannan alkaluman za su rika karuwa a kai a kai, kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS zai kara karfafa har zai samu babban sakamako, Zhang Yansheng ya bayyana cewa, ganawar shugabannin kasashen karo na 9 mai taken "zurfafa huldar abokantaka dake tsakanin kasashen BRICS, tare kuma da samun makoma mai haske" da za a gudanar a birnin Xiamen za ta bude wani sabon shafi ga tsarin hadin gwiwar kungiyar a cikin shekaru goma masu zuwa, ya ce, babban taken taron yana kunshe da fannoni hudu, ya ce, "Na farko, kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasashen BRICS domin samun ci gaba tare, hakan ana iya cewa, ana fatan za a habaka hadin gwiwa dake tsakanin kasashen duniya ta hanyar kara karfafa huldar abokantaka a fannin tattalin arziki tsakanin kasashen BRICS, na biyu, kara kyautata tsarin kasa da kasa domin tunkarar kalubale tare, wato kamata ya yi kasashen BRICS su yi kokarin kiyaye zaman lafiya a fadin duniya, tare kuma da kyautata tsarin harkokin kudi, na uku, kara gudanar da cudanyar al'adu domin cimma ra'ayi daya kan harkokin kasa da kasa a fadin duniya, musamman a fannonin ba da ilmi da wasannin motsa jiki, na hudu, kara mai da hankali kan batun bullo da tsarin sada zumunta a fadin duniya."

Rahotanni na cewa, yayin taron ministocin tattalin arziki da cinikayyar kasashen BRICS da aka kira a farkon watan da muke ciki, an sanya hannu kan wasu takardun guda takwas dake shafar hadin gwiwa a fannin ciniki tsakaninsu, mataimakin darektan hukumar ilmi na cibiyar nazarin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki ta ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Zhang Jianping ya nuna cewa, ganawar shagabannin kasashen BRICS karo na 9 da za a gudanar za ta kara mai da hankali kan batun zuba jari, ya ce, "Babban taken ganawar shi ne kara karfafa huldar abokantaka domin gudanar da hadin gwiwa yadda ya kamata, ana sa ran cewa, za a kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa daga dukkan fannoni, musamman ma a fannin zuba jari, dalilin da ya sa haka shi ne domin hadin gwiwar tattalin arziki za ta samar da dama ga kasashen BRICS domin su samu ci gaba."

A sa'i daya kuma, za a bullo da wani sabon tsarin hadin gwiwa a yayin ganawar shugabannin a Xiamen wato ana fatan za a kara shigo da wasu sauran kasashen duniya cikin tsarin hadin gwiwar, misali kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki, ko kasashe masu tasowa, mataimakin darektan hukumar raya ilmi na cibiyar nazarin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki ta ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Zhang Jianping ya yi mana bayani cewa, tsarin da za a aiwatar ya alamta cewa, tsarin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen BRICS zai bude kofa ga daukacin kasashe masu tasowa, yana mai cewa, "Tsarin hadin gwiwa dake tsakanin BRICS yana shafar kasashe masu tasowa, kuma ayyuka masu muhimmanci dake gabansu su ne yaki da talauci da raya masana'antu da kyautata muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da kuma shiga hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa da ke dace da yanayin kasashensu domin samun ci gaba, to, idan ana son cimman wannan burin, dole kasashen BRICS su hada kai tare da sauran kasashe masu tasowa."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China