in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Afirka ta Kudu suna fatan kasashen BRICS za su kara karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka
2017-08-25 11:07:54 cri

A karshen shekarar 2010, aka shigar da kasar Afirka ta Kudu cikin kungiyar kasashen BRICS, daga lokacin ne kuma a hukumance ta fara shiga tsarin hadin gwiwa dake tsakanin wadannan kasashen wakilan kungiyar, kawo yanzu shekaru shida ke nan. To ko wane irin tasirin wannan tsari ya yi ga kasar ta Afirka ta Kudu?

A karshen shekarar 2010, aka shigar da Afirka ta Kudu cikin kungiyar BRICS, ta kuma kasance kasa daya tilo a nahiyar Afirka wadda take halartar tsarin hadin gwiwa na kungiyar. Kwararre mai nazarin huldar dake tsakanin kasa da kasa na Afirka ta Kudu Francis Kornegay yana ganin cewa, lamarin ya kara karfafa matsayin kasar na ba da jagoranci kan ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka. Ya ce, "Ko shakka babu Afirka ta Kudu ta kara haifar da tasiri ga ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afirka, tun bayan shigar ta kungiyar BRICS, hakan ya sake gaskata cewa, kasar na taka muhimmiyar rawa daga duk fannoni a fadin nahiyar Afirka. Kana an zabe ta domin kafa hedkwatar bankin raya kasashen BRICS dake Afirka, wanda hakan ma alama ce, ta cewa Afirka ta Kudun na da muhimmanci matuka a nahiyar, musamman ma wajen raya tattalin arziki."

Darektan cibiyar nazarin kasashen BRICS ta kwamitin nazarin al'adu da kimiyya na Afirka ta Kudu Jaya Josie ya bayyana cewa, kasar Afirka ta Kudu ta samu wata sabuwar damar kara kyautata huldar dake tsakaninta da kasashen waje, tun bayan da ta shiga kungiyar BRICS, yana mai cewa, "Shiga kungiyar BRICS yana da muhimmanci matuka ga kasar ta Afirka ta Kudu, saboda hakan ya samar da wata sabuwar dama gare ta, ta kara kyautata huldar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, misali daga kasashe masu ci gaba zuwa kasashe mafiya saurin samun ci gaban tattalin arziki."

Kwararre kan tattalin arziki da diplomasiyya dake aiki a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Afirka ta Kudu Cyril Princeloo na ganin cewa,

Afirka ta Kudu ta samu sabuwar abokiyar ciniki ta hanyar shiga kungiyar BRICS, ya ce, "Bayan da kasar Afirka ta Kudu ta shiga kungiyar BRICS, ta sake samun wasu abokan ciniki, tare kuma da samun sabuwar kasuwa, a bayyane take cewa, adadin cinikin dake tsakaninta da sauran kasashe wakilan kungiyar BRICS ya karu bisa babban mataki, musamman ma tsakaninta da kasar Sin, kuma hakan ya sa kaimi sosai ga ci gaban tattalin arzikin Afirka ta Kudu."

Bisa matsayinta na kasar dake cikin kungiyar BRICS daya tilo a nahiyar Afirka, har kullum Afirka ta Kudu tana mai da hankali kan aikin kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da kasashen Afirka, da ma kara kyautata tsarin hadin gwiwa da huldar abokantaka, wanda zai kasance muhimmin batu da za a tattauna a kai, yayin ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 9 da za a gudana a birnin Xiamen dake lardin Fujian na kasar Sin. Game da ganawar da za a yi, kwararre mai nazarin huldar dake tsakanin kasa da kasa na Afirka ta Kudu Francis Kornegay ya bayyana cewa, yana fatan za a kara raya huldar abokantaka dake tsakanin kasashen BRICS da kasashen Afirka, ya ce, "Ina tsammanin cewa, ganawar shugabannin kasashen BRICS da aka shirya a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2013 ta samu wani babban sakamako, wato ta tabbatar da cewa, za a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da kasashen Afirka, wajen ciyar da kasashen Afirka gaba yadda ya kamata, kuma a yanzu ba a tsara hakikanin shirin hadin gwiwa tsakaninsu ba tukuna, shi ya sa kamata ya yi kasar Afirka ta Kudu ta kara ba da muhimmanci kan wannan batu."

Darektan cibiyar nazarin kasashen BRICS ta kwamitin nazarin al'adu da kimiyya na Afirka ta Kudu Jaya Josie yana ganin cewa, idan ana son cimma wannan buri, dole ne a kara karfafa cudanyar al'adu tsakanin sassan biyu.

Kwararre kan tattalin arziki da diplomasiyya dake aiki a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Afirka ta Kudu Cyril Princeloo yana fatan kasashen BRICS za su kara zuba jari a kasashen Afirka domin kyautata tsarin ciniki a nahiyar, ya ce, "Na luar da cewa kasar Sin ta kafa wasu kamfanoni da dama a kasashen Afirka, hakan zai taimaka matuka ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar, ina fatan kasashen BRICS za su kara zuba jari a sana'oin sarrafa kayayyaki a kasashen Afirka, a maimakon fitar da kayan da ake bukata domin sarrafawa."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China