in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfin kirkiro kasashen BRICS ya karu sosai
2017-08-30 11:46:18 cri

A tsakanin ranakun 3 da 5 ga watan Satumban bana, za a yi taron shugabannin kasashen BRICS karo na 9 a birnin Xiamen dake gabashin kasar Sin. Yanzu, kasashen BRICS sun kasance kashin bayan ci gaban kasashe masu tasowa wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani, kana ginshikin kirkiro sabbin fasahohin zamani a duk fadin duniya. A jiya Talata ne, cibiyar kula da harkokin cudanyar fasahohin kimiyya ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto, inda ta bayyana cewa, yawan kudin da kasashen BRICS suka zuba a fannin harkokin kirkiro sabbin fasahohin zamani ya kai kashi 17 cikin dari bisa na dukkan kasashen duniya. Wannan ya alamta cewa, gudummawar da kasashen BRICS suke bayarwa harkokin kirkiro sabbin fasahohin zamani a duniya tana karuwa a kai a kai.

Cibiyar kula da harkokin cudanyar fasahohin kimiyya ta kasar Sin ce ta hada kan kwararru kusan 40 na kasar Sin da na kasashen waje, ciki har da jami'ar koyon ilmin tattalin arziki ta kasar Rasha, inda suka tsara wannan "Rahoto kan yadda kasashen BRICS suke kara karfinsu na takara a fannin kirkiro sabbin fasahohin zamani". Bisa rahoton, idan an kwatanta kasashen BRICS da sauran kasashen duniya a fannin kirkiro sabbin fasahohin zamani, za a fahimci cewa, yawan kudin da kasashen BRICS suka zuba ya kai kashi 17 cikin dari bisa na duk duniya, yawan kudin kayayyaki a fannin fasahohin zamani da suke fitarwa zuwa sauran kasashen duniya ya kai dalar Amurka biliyan dubu 6, wato ya kai kashi 28 cikin dari bisa na duk duniya. Sannan yawan bayanan kimiyya da fasaha da masana da kwararru na kasashen BRICS suka wallafa ya kai dubu 590, wato ya kai kashi 27 cikin dari bisa na duk duniya. Mr. Zhao Xinli, mataimakin shugaban cibiyar kula da harkokin cudanyar fasahohin kimiyya ta kasar Sin, kuma mamban kwamitin tsara wannan "Rahoto kan yadda kasashen BRICS suke bunkasa karfinsu na takara a fannin kirkiro sabbin fasahohin zamani" yana mai cewa, wannan kididdiga ta alamta cewa, kasashen BRICS na bayar da karin gudumawa ga duk kasashen duniya a fannin nazarin kimiyya da kirkiro sabbin fasahohin zamani a kai a kai, tasirinsu a duniya ma ya karu cikin sauri. Yanzu dukkan kasashen BRICS sun zama abin koyi a yankunan da suke.

Bugu da kari, wannan rahoto yana ganin cewa, a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2016, karfin takara na kirkiro sabbin fasahohin zamani da kasashen BRICS suke da shi ya karu, a cikinsu, kasashen Sin da Rasha su ne a kan gaba, sannan kasar Indiya tana matsayi na uku, yayin da kasashen Brazil da Afirka ta kudu suke samun ci gaba sannu a hankali.

Bisa ci gaban da ake fatan za su samu a nan gaba, wannan rahoto ya yi hasashen cewa, karfin kirkiro sabbin fasahohin zamani na kasashen BRICS zai ci gaba da karfafuwa. Mr. Zhao Xinli yana mai cewa, "Ya zuwa shekara ta 2030, karfin kirkiro sabbin fasahohin zamani na kasashen BRICS zai kara karfafuwa, kana kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa a kan gaba. Kana ya zuwa shekara ta 2030, karfin kirkiro sabbin fasahohin zamani da kasar Sin take da shi zai kai matsayi na uku a duk fadin duniya."

Yayin da kasar Sin ke yin hadin gwiwa da sauran kasashen BRICS a fannin kirkiro sabbin fasahohin zamani, hankalin wadannan kasashe ya fi karkata kan fannonin ayyukan kirkiro sabbin fasahohin zamani na kasa da kasa, da kafa cibiyoyin musayar masana da kwararru. Alkalumu sun nuna cewa, a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, yawan ayyukan kirkiro sabbin fasahohin zamani da kasar Sin da sauran kasashen BRICS suka yi cikin hadin gwiwa ya kai 665, inda ta kashe kudin RMB biliyan 2.729. Bugu da kari, yawan ayyuka da kudi da kasar Sin ta kebe dukkansu sun karu a kowace shekara. Sannan, yawan cibiyoyi kirkiro sabbin fasahohin zamani da kasar Sin da sauran kasashen BRICS suka kafa cikin hadin gwiwa ya kai 190. Mr. Zhao Xinli yana ganin cewa, irin wannan hadin gwiwa a fannin kirkiro sabbin fasahohi tana da amfani.

"Alal misali a fannin yada fasahar zamani ta yau da kullum, jami'ar koyon ilimin labarin kasa ta kasar Sin ta taimakawa jihar West Bengal ta kasar Indiya a fannin tsabtace ruwan dake karkashin kasa mai zurfi. An yi shekaru 10 ana gudanar da wannan aiki a kasar Indiya, inda aka warware matsalar gurbata ruwan dake karkashin kasa mai zurfi."

Sannan wannan rahoto ya ba da shawara cewa, a nan gaba, ya kamata kasashen BRICS su kara yin hadin gwiwa wajen daidaita batutuwa da kara yin mu'amala tsakanin masana da kwararru, da kuma kafa dandalin musayar fasahohin zamani tsakaninsu da dai makamatansu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China