in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya ce kasarsa za ta karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS
2017-09-01 10:17:50 cri

Kwanakin baya ne, shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi wanda zai zo birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin don halartar taron shugabannin kasashen BRICS karo na tara ya zanta da manema labaran kafofin watsa labarai na kasar Sin a Alkahira, babban birnin kasar Masar, inda ya bayyana cewa, kasashen wakilan kungiyar BRICS suna taka muhimmiyar rawa a dandalin siyasar duniya, kuma kasarsa za ta himmatu domin kara ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasashen, tare kuma da ciyar da tattalin arzikinsu gaba.

Da farko shugaba Sisi ya nuna godiyarsa matuka ga shugaban kasar Sin Xi Jinping bisa ga gayyatar da ya yi masa domin ya halarci taron shugabannin kasashen BRICS karo na tara da za a gudanar a birnin Xiamen, kana ya isar da gaisuwa ga al'ummar kasar ta Sin. Shugaba Sisi ya yi nuni da cewa, yanzu haka adadin GDP na kasashen BRICS ya kai kaso 22 bisa dari daga cikin daukacin adadin GDP na duniya, adadin al'ummomin kasashen shi ma ya kai kaso 40 bisa dari, ko shakka babu kasashen suna taka muhimmiyar rawa a dandalin siyasar duniya, kana tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS yana taimakawa ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da kasashen BRICS, shi ya sa yana ganin cewa, halartar taron shugabannin kasashen BRICS da Masar za ta yi, yana da babbar ma'ana, saboda Masar za ta nuna muhimmancinta kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS.

Shugaba Sisi yana fatan cewa, Masar za ta samu damar yin tattaunawa da kasashen BRICS domin kara zurfafa fahimtarsa a kan batututan dake shafar bunkasar kasashe masu tasowa da kalubalen da suke fuskanta a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma zaman takewar al'umma. Ya gaya wa manema labaran kasar Sin cewa, yayin taron da za a gudanar, za a shirya wani dandalin kasuwanci da masana'antu, inda za a nuna wa gwamnatin Masar matakan da kasashen suka dauka wajen yin kwaskwarimar tattalin arziki a cikin 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin Masar ita ma za ta nuna musu matakan da take dauka don taimaka wa aikin shigo da jarin waje, misali kafa sabuwar dokar zuba jari wadda za ta samar da manufofin gatanci ga 'yan kasuwar kasashen waje da su zuba jari a kasar ta Masar.

A game da batun rawar da kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa suke takawa a cikin harkokin kyautata tsarin tattalin arziki a fadin duniya kuwa, shugaba Sisi ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu ya dace kasashe masu tasowa su kara mai da hankali kan wannan batun, ta haka ba za a yi watsi da bukatunsu ba, maimakon kasashe masu ci gaba su yi la'akari kan moriyarsu kawai. Sisi yana ganin cewa, kamata ya yi kasashe masu tasowa su kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu domin bullo da wata dabarar raya al'adu da tattalin arziki da ta dace.

Ziyarar da Sisi zai kawo kasar Sin, ita ce karo na hudu a matsayinsa na shugaban kasar Masar, ya ce, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 1956, sassan biyu suna gudanar da huldar yadda ya kamata har ta kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya, musamman ma a Asiya da kuma Afirka.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, huldar dake tsakanin Sin da Masar ta shiga wani sabon matsayi, inda ta samu sabon ci gaba. A shekarar 2014, kasashen biyu sun kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, kana a watan Janairun shekarar 2016 da ta gabata, sassan biyu sun bullo da "shirin gudanar da huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga duk fannoni a tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru biyar masu zuwa."

Shugaba Sisi ya bayyana cewa, yayin da yake ziyara a kasar Sin, zai yi shawarwari da shugaba Xi domin tattauna batutuwan da suka fi jawo hankulansu duka, tare kuma da kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu, misali kara sa kaimi kan kamfanonin kasar Sin domin su ci gaba da gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, da kuma gudanar da wasu ayyukan samar da wutar lantarki da makamashi da sufuri da sauransu a Masar.

Kazalika, shugaba Sisi ya jaddada cewa, kasarsa ta nuna fiffiko yayin da ake kokarin aiwatar da shirin "ziri daya da hanya daya", a saboda haka yana fatan kasashen biyu za su kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China