in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Xi Jinping ya jaddada aniyar Sin ta tabbatar da nasarar gasar Olympic ta hunturun shekarar 2022
2017-08-31 10:51:36 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa kasar sa za ta tsara, tare da aiwatar da dukkanin matakai da suka wajaba, don ganin gasar Olympic ta yanayin hunturu ta shekarar 2022 da za ta karbi bakunci ta gudana cikin nasara.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne, yayin da yake zantawa da shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa (IOC) Mr. Thomas Bach, wanda ke cikin manyan bakin da aka gayyata, a bikin bude babbar gasar wasanni karo na 13 na kasar Sin a birnin Tianjin.

Xi ya ce tuni aka yi nisa da shirye shirye, kuma sin za ta cika alkawarin da ta dauka na shirya kasaitacciyar gasa a shekarar ta 2022. Kaza lika kasar za ta yi kyakkyawan amfani da damammakin dake kunshe cikin gasar, wajen bunkasa wasannin lokacin hunturu tsakanin al'ummar ta, ta yadda hakan zai bude karin kofofi na inganta lafiyar Sinawa.

Da yake maraba da zuwan Mr. Bach, shugaba Xi ya jinjinawa hukumar IOC, da shi kan sa jagoran na ta, game da kokarin sa na bunkasa sha'anin wasanni a Sin. Ya ce Sin na matukar martaba wasanni, da gasar Olympic a matsayin dama ta bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Shugaba Xi ya ce kasar sa za ta ci gaba da baiwa IOC goyon baya cikin muhimman ayyukan ta, na raya wasanni, da bunkasa hadin kai, da wanzar da zaman lafiya a duniya baki daya, tare da raya sha'anin wasanni a duniya duka.

A sana bangare kuwa Mr. Bach cewa ya yi, ziyarar da shugaba Xi ya kai helkwatar IOC dake birnin Lausanne na Switzerland, a watan Janairun farkon shekarar nan ya ja hankulan duniya baki daya.

Hakan a cewar sa ya shaida yadda kasar Sin, da jama'ar ta ke kimanta damar su ta karbar bakuncin gasar Olympic na shekarar 2022 dake tafe. Ya ce ga dukkanin alamu, Sin za ta gudanar da gasar a yanayin muhalli mai tsafta, da kayatarwa, tare da amfani da fasahohi na zamani, wadanda za su bada damar cimma nasarar gasar yadda ya kamata. Mr. Bach ya kara da cewa, kwamitin IOC zai yi hadin gwiwa da Sin, wajen ganin an cimma burin da aka sanya gaba a wannan fanni.

Ita dai wannan babbar gasa da kasar Sin ke shiryawa tun daga shekarar 1959, na ci gaba da janyo hankulan duniya, inda 'yan wasa daga yankuna da lardunan kasar ta Sin daban daban ke halarta. Mashiryan ta sun bayyana cewa, cikin kwanaki 12 da za a shafe ana gudanar da gasar, 'yan wasa 12,721 za su shiga a dama da su, a rukunonin wasanni 33 masu kunshe da sassa 417.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China