Saina Nehwal ta samu kuri'u 1233 a zaben, wadda hakan ya sa ta zama a matsayi na shida, a matsayin sabuwar mambar kwamitin 'yan wasan na IOC na wannan karo. Sauran sabbin membobin kwamitin biyar sun hada da dan wasan kwallon tebur na kasar Koriya ta Kudu Ryu Seung-min, da 'yar wasan takobi ta kasar Jamus Britta Heidemann, da dan wasan iyo na kasar Hungary Daniel Gyurta, da 'yar wasan tsalle ta hanyar amfani da sanda ta kasar Rasha Yelena Isinbayeva, da kuma 'yar wasan keke ta kasar New Zealand Sarah Walker.
A watan Afrilun shekarar 2015 ne aka gabatar da sabon jerin sunayen 'yan wasan kwallon badminton mata mafi kwarewa a duniya, inda Nehwal ta maye gurbin 'yar wasan kasar Sin Li Xuerui, a matsayin zakara a jerin sunayen. A kuma wannan karo ne ta fara zama 'yar wasan kwallon badminton daga kasar Indiya ta farko da ta kai matsayin farko a duniya.
A halin yanzu, Nehwal din ce ke matsayi na biyar a duniya, kuma ba ta samu lambar yabo a gasar wasannin Olympics a Rio ba saboda rauni da ta ji.
Kwamitin 'yan wasannin na Olympic, kwamiti ne na musamman dake karkashin jagorancin kwamitin na IOC, yana kuma kunshe da mambobi 'yan wasa 12. A kan zabi mambobin sa a yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ko ta sanyi. Kuma a wannan karo, an zabi sabbin membobin kwamitin guda shida. (Zainab)