Wata sanarwa da ma'aikatar wasannin ta fitar, ta ce an karya matsayin bajimta a wasannin motsa jiki 12, da kuma daya a gasar linkaya, sai kuma daya a wasan harbin bindiga. 'Yan wasa 266 ne dai suka kara a gasar ta birnin Moscow, a rukunin wasannin da suka gudana tsakanin ranekun 7 zuwa 10 ga watan nan na Satumba.
A ranar 7 ga watan Agusta ne dai kwamitin tsara gasar Olympic ajin nakasassu na kasa da kasa, ya tabbatar da dakatar da 'yan wasan na Rasha daga shiga gasar birnin Rio, bisa rahoton da hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta duniya ta fitar, wanda ya zargi hukumomin Rashan da baiwa 'yan wasan kasar masu ta'ammali da irin wadannan kwayouyi kariya.
Kwamitin shirya gasar Olympic ajin nakasassu na Rashan ya yi yunkurin daukaka kara game da wannan hukunci, sai dai hakar sa bata cimma ruwa ba. Bisa hakan ne kuma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya sanar da kudurin gwamnatin sa, na shirya wata gasa ta musamman a cikin kasar, domin maye gurbin wadda aka hana 'yan wasan kasar shiga.(Saminu Alhassan)