in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Sojojin India da suka shiga yankin Dong Lang (Dok Lam) na Sin sun janye
2017-08-28 16:36:13 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta tabbatar a yau Litinin cewa, da yammacin yau ne India ta janye baki dayan sojoji da na'urorinta daga iyakar dake tsakaninta da Sin, bayan da suka sun tsallaka zuwa yankin Dong Lang (Dok Lam) na Sin ba bisa doka ba. Kasar Sin ta tabbata haka bayan bincike a wurin.

A sa'i daya kuma, ma'aikatar harkokin wajen Sin ta jaddada cewa, kasar za ta tabbatar da 'yancinta na mallakar yankunanta kamar yadda aka shata kan iyaka.

A ranar 18 ga watan Yuni ne. Sojojin tsaron iyaka na kasar India suka tsallaka sashen iyakar Sikkim dake tsakanin Sin da India har suka shiga yankin Dong Lang (Dok Lam) na kasar Sin. Kasar Sin ta shan yin tattaunawar diflomasiya da India, ta kuma bayyana hakikanin halin da ake ciki ga kasashen duniya, kana ta bayyana matsayi mai tsauri da take dauka da bukatunta, inda ta kalubalanci India da ta fice daga yankin ba tare da bata lokaci ba. A sa'i daya kuma sojojin kasar Sin sun dauki matakai masu karfi, don kiyaye 'yanci da muradun kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China