in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD: An samu cigaba a tattaunawar sulhu a Sudan ta kudu, amma akwai kalubale
2017-08-25 12:25:12 cri
Mataimakin sakatare janar na MDD kan shirin wanzar da zaman lafiya, El Ghassim Wane, ya fada a ranar Alhamis cewa, an samu cigaba a tattaunawar zaman lafiya a Sudan ta kudu, sai dai har yanzu akwai wasu manyan kalubaloli da ake fuskanta game da ceton yankunan da ke fama da tashin hankali.

Jami'in ya nanata cewa, matsalar tashin hankalin Sudan ta kudu dan adam ne ya haddasa ta, inda ya zargi shugabannin kasar da cewa su ne ke da alhakin haddasa rikicin kasar.

Sai dai Wane, ya bayyanawa kwammitin tsaron MDD game da halin da ake ciki kan rikicin Sudan ta kudu cewa, shugabannin kasar ne ya dace su sake mayar da kasar kan turbar zaman lafiya.

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, shi ne ya kaddamar da shirin tattaunawar zaman lafiyar kasar a bara, inda ya bayyana matakin da cewa, zai iya kawo karshen yakin basasar kasar, kana zai iya magance wasu manyan matsaloli dake addabar kasar.

Ya ce babban abin da ake bukata shi ne, yin amfani da matakai na siyasa don dakatar da amfani da karfin soji, domin tattaunawar sulhu, da kuma cimma daidaito don samun zaman lafiya mai dorewa a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China