in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na horas da jami'ai a Sudan ta Kudu game da kula da 'yan gudun hijira
2017-06-30 09:27:38 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, da hadin gwiwar takwarar ta ta CRA, sun bude wani taro domin horas da jami'ai a Sudan ta Kudu game da ayyukan tallafawa 'yan gudun hijira.

Yayin taron na yini biyu, jami'an hukumomin sun nusar da ma'aikatan gwamnatin Sudan ta kudun, hanyoyin kare hakkin bil adama da na kare 'yan gudun hijira.

Wata sanarwa da hukumar ta UNHCR ta fitar ta bayyana cewa, taron horaswar ya hada manyan jami'an gwamnati, da masana, tare da kwararru, inda suka yi musayar fahimta don gane da hanyoyin magance matsaloli, musamman wadanda ake fuskanta a sansanonin 'yan gudun hijira.

Da take tsokaci game da hakan, mataimakiyar wakilin hukumar UNHCR sashen ba a kariya ga 'yan gudun hijira a kasar Maria Corinna Miguel-Quicho, ta ce baiwa 'yan gudun hijirar kariya, aiki ne mai matukar muhimmanci ga kasashen duniya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China