in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta bukaci bangarorin dake takaddama a Sudan ta Kudu su amince da yarjejeniyar zaman lafiya
2017-06-13 10:01:45 cri

Shugabannin kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika IGAD sun bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Sudan ta Kudu da su amince da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

Shugabannin na gabashin Afrika suna tattaunawa ne game da halin da ake ciki a Sudan ta Kudun a yayin ganawarsu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda suka bukaci bangarorin biyu da su mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattaba hannu a kanta a shekarar 2015 a Addis Ababa.

Firaiministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn, wanda shi ne shugaban taron na IGAD, a cikin jawabinsa na bude taron shugabannin na IGAD karo na 31, da kuma taron koli na shugabannin gwamnatoci a ranar Litinin ya tabbatar da cewa, amfani da matakin soji ba zai iya magance rikicin na Sudan ta Kudu ba.

A shekarar 2015 aka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya kan rikicin Sudan ta Kudu a Addis Ababa wadda ba ta yi nasara ba, amma a watan Yulin shekarar 2016, an sake samun barkewar sabon tashin hankali. Sudan ta Kudu ta afka cikin yakin basasa ne tun a watan Disambar shekarar 2013.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China